Wani sabon rikici ya sake kunno kai a jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, bayan dan takarar gwamna, Mista Maurice Vunobolki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar tare da wasu dimbin magoya bayansa.
Vunobolki ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Yola ranar Talata, inda ya ce ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne bayan dogon nazari da tuntuba da masu ruwa da tsaki a jihar.
Ya zargi shugabannin jam’iyyar da kokarin kakaba dan takara maimakon gudanar da sahihin zaben fidda gwani, yana mai cewa hakan na nuna alamun rashin gaskiya da adalci a tsarin siyasar jam’iyyar.
A cewarsa, akwai alamun da ke nuna cewa ana son cimma matsaya ta hanyar da ba ta dace ba, maimakon bin hanyoyin dimokuradiyya da suka dace, wanda hakan ka iya haifar da rikici a gaba.
Haka kuma, ya zargi Gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri, da gaza cika alkawarin tabbatar da gaskiya da adalci a zaben fidda gwani, duk da cewa ya taba bayar da tabbacin hakan.
Vunobolki ya kuma yi zargin cewa akwai sahihan hujjoji na yin rajistar mambobi ba bisa ka’ida ba, inda ake amfani da lambobin NIN na mutane ba tare da izininsu ba domin kara yawan masu kada kuri’a a wasu yankuna.
Daga karshe, ya bukaci dukkan magoya bayansa a kananan hukumomi 21 na jihar su fice daga APC, yana mai cewa za su sanar da mataki na gaba nan gaba, domin neman wata sabuwar hanya mai gaskiya da adalci a harkokin siyasa.
