Gwamnatin Nijeriya ta kashe kimanin naira biliyan 418.79 a matsayin tallafin wutar lantarki a zangon karshe na shekarar 2025, kamar yadda sabon rahoton Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya NERC ta nuna.
Rahoton ya bayyana cewa adadin ya ragu da kusan naira biliyan 39.96 idan aka kwatanta da zango na uku na shekarar, inda aka kashe naira biliyan 458.75. Tallafin da gwamnati ta sanya ya kai kashi 52.30 cikin 100 na kudin da kamfanonin samar da wuta (GenCos) suka bukata, wanda ya ragu daga kashi 58.63 a zangon da ya gabata.
Rahoton ya kara da cewa Kamfanin cinikayyar wutar lantarki na Nijeriya (NBET) ya fitar da takardun biyan kudi ga kamfanonin rarraba wuta (DisCos) da suka kai naira biliyan 386.13 bayan da aka dai-dai, yayin da kamfanin DisCos suka biya naira biliyan 359.27, wato kashi 93.04 cikin 100 na abin da ake bukata na tallafin.
Rahoton ya danganta raguwar tallafin da karin yawan wutar da aka ware wa masu amfani da Band A daga kashi 40 zuwa 45, matakin da gwamnati ke dauka domin inganta wutar da ake bai wa kwastomomi.
Sai dai rahoton ya nuna cewa ba duka DisCos ne suka cika biyan kudadensu ba, inda kamfanonin Kano, Jos da Kaduna suka nuna karancin biyan kudi, yayin da wasu kamar Abuja, Lagos, Enugu, Ikeja da Port Harcourt suka ci gaba da biyan kashi 100 cikin 100.
Hukumar ta jaddada cewa gwamnati na ci gaba da ɗaukar nauyin gibin da ke tsakanin farashin wuta da wanda aka amince da shi, domin saukaka wa jama’a, duk da cewa hakan na kara nauyi ga kasafin kuɗin kasa.
