DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 14, 2026
HomeLabaraiAdadin fetur da ake shigowa da shi Nijeriya ya karu a watan...

Adadin fetur da ake shigowa da shi Nijeriya ya karu a watan Maris – NMDPRA

Shigo da man fetur a Nijeriya ya karu da kusan kashi 96.7 cikin dari a watan Maris 2026 idan aka kwatanta da watan Fabrairu, kamar yadda rahoton hukumar kula da albarkatun mai ta Nijeriya NMDPRA ta bayyana.

Rahoton ya nuna cewa yawan fetur da ake shigowa da shi ya tashi daga lita miliyan 3 a rana zuwa lita miliyan 5.9 a rana, yayin da samar da fetur a cikin gida, ciki har da na matatar man Dangote ya karu daga lita miliyan 30.5 zuwa miliyan 34.2 a rana.

Gaba daya, jimillar fetur da ake samu a kullum ya ɗan ƙaru daga lita miliyan 39.5 zuwa miliyan 40.1, sai dai amfani da fetur ya ragu daga lita miliyan 56.9 zuwa miliyan 47.3 a rana, abin da ke nuna raguwar buƙata sakamakon tsadar farashi.

Sai dai rahoton ya nuna cewa ajiyar fetur ya ragu daga kwanaki 30 zuwa kwanaki 21, alamar cewa duk da ƙarin shigo da fetur, har yanzu akwai matsin lamba a sarkar samar da man.

Hukumar ta ce duk da ƙoƙarin rage dogaro da fetur na waje, an sake bai wa ‘yan kasuwa lasisin shigo da mai domin kauce wa ƙarancin kaya yayin da ake ƙara ƙarfafa matatun cikin gida.

Haka kuma, rahoton ya nuna cewa samar da dizal ya ragu sosai, yayin da iskar gas ta ɗan ƙaru, lamarin da ke nuna sauye-sauye a ɓangaren makamashi.

Masana sun ce haɗin gwiwar ƙaruwa a samar da fetur a gida da kuma faɗaɗa matatun mai na iya rage dogaro da shigo da mai a nan gaba, tare da ƙarfafa ɓangaren makamashi a Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata