DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, May 16, 2026
HomeLabaraiMakarantar kwana ta biliyan 1 a Sokoto na nan a rufe shekaru...

Makarantar kwana ta biliyan 1 a Sokoto na nan a rufe shekaru 9 bayan kammalawa

Makarantar kwana ta zamani da ke Balle a ƙaramar hukumar Gudu ta jihar Sokoto ta ci gaba da kasancewa a rufe tsawon shekara tara bayan kammala aikinta.

An gina makarantar ne a shekarar 2017 a zamanin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, a wani yunƙuri na magance matsalolin ilimi da ke addabar al’ummomin yankunan kan iyaka na ƙaramar hukumar.

Rohotanni sun nuna Gudu a matsayin ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin jihar Sokoto da ke fama da ƙarancin makarantu masu inganci na sakandare, lamarin da ya sa iyaye da dama ke wahalar da kansu wajen kai ’ya’yansu makarantu a garuruwa masu nisa, yayin da wasu ɗaliban kuma suka daina karatu gaba ɗaya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, makarantar wadda aka ce an kashe kusan naira biliyan ɗaya wajen gina ta, ta ƙunshi azuzuwa, ɗakunan kwanan ɗalibai, asibiti, masallaci, hanyoyin shiga makarantar da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa.

A lokacin bikin ranar dimokuraɗiyya na shekarar 2016, Tambuwal ya bayyana cewa makarantar za ta taimaka wajen ƙara yawan ɗaliban da ke shiga makaranta tare da rage yawan waɗanda ke barin makaranta kafin kammala karatu a Gudu da maƙwabtan ƙananan hukumomi.

“Tabbas duk da ƙoƙarin gwamnatoci daban-daban, matakin bunƙasar ilimi a Gudu ya kasance mafi ƙasa a jihar,” in ji tsohon gwamnan a lokacin.

An kuma tsara makarantar domin karɓar ɗalibai daga al’ummomin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, inda aka tsara koyar da darussa cikin harshen Turanci da Faransanci.

Sai dai shekara tara bayan kammala aikin makarantar, har yanzu ba a fara karatu ba, kuma babu wani ɗalibi da aka taɓa ɗauka.

A halin yanzu jami’an tsaro ne ke amfani da harabar makarantar sakamakon matsalar tsaro da yankin ke fuskanta.

Sai dai mazauna yankin sun musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa al’umma na son a mayar da makarantar sansanin soji na dindindin.

Wani mazaunin yankin, Malam Umar Balle, ya ce al’umma na yaba wa jami’an tsaro saboda rawar da suke takawa, amma ya jaddada cewa makarantar an gina ta ne domin amfanin yara.

“Ba mu da matsala da sojoji domin tsaro yana da muhimmanci a gare mu. Amma an gina wannan makaranta ne domin yaranmu kuma har yanzu muna buƙatarta.

“Muna roƙon gwamnati ta samar wa jami’an tsaro wani wuri dabam sannan makarantar ta fara aiki,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa tsarin ginin makarantar ya dace har ma a mayar da ita cibiyar ilimi mai zurfi idan gwamnati ba za ta iya buɗe ta a matsayin makarantar sakandare ba.

“Muna son gwamnatin jihar ta dawo da makarantar yadda aka tsara ko kuma ta mayar da ita wata kafa ta Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Gidan Madi ko wata jami’a domin kada kayan aikin su lalace babu amfani,” in ji shi.

Ya bayyana cewa duk da an ɗaga darajar makarantu kamar GDSS Balle da GDSS Kurdula da GDSS Bacaka domin bayar da shaidar SSCE, al’umma har yanzu na ganin makarantar kwana ta Balle a matsayin babban aikin ilimi da yankin ke buƙata.

Shugaban ƙungiyar ɗaliban Gudu (GULSA), Ahmad Usman Jimajimi, ya ce kafin yanzu ɗalibai daga yankin kan je makarantu a Gidan Madi da Nagarta College da Sheikh Abubakar Gummi da kuma FGC Sokoto saboda rashin makarantu kusa da su.

“Wasu iyaye ba za su iya ɗaukar nauyin tura ’ya’yansu wajen yankin ba, hakan ya sa ɗalibai da dama suka hakura da karatu gaba ɗaya,” in ji shi.

Ya ce sake buɗe makarantar zai taimaka wajen bunƙasa ilimi tare da rage matsalolin tsaro ta hanyar ba matasa ilimi da cigaba.

“Duk yadda gwamnati ke son magance matsalar tsaro, dole ilimi ya kasance cikin mafita,” in ji shi.

Shi ma shugaban kwamitin kula da makarantu na ƙaramar hukumar Gudu, Attahiru Balle, ya roƙi gwamnati kada ta bari gine-ginen makarantar su lalace.

“An gina wannan makaranta ne domin sauya tarihin ilimi a wannan yankin. Muna roƙon gwamnati ta buɗe ta domin amfanin yaranmu,” in ji shi.

Hakazalika, shugaban gargajiyar yankin, Aminu Aliyu (Sarkin Yamman Balle), ya ce an kafa makarantar ne domin hidimtawa al’ummomin kan iyaka kafin matsalar tsaro ta dakatar da shirin.

“Makarantar har yanzu tana cikin yanayi mai kyau. Abin da muke so shi ne gwamnati ta samar wa jami’an tsaro wani sansani dabam sannan ɗalibai su fara karatu a nan,” in ji shi.

Da aka tuntubi kwamishinan yaɗa labarai na jihar Sokoto, Bello Sambo Danchadi, ya ce gwamnati za ta yi duk abin da ya dace domin amfanin jama’a.

“Gwamnatin jihar gwamnati ce ta jama’a, kuma za ta yi abin da ke da amfani ga al’umma. Da zarar matsalar tsaro ta lafa, makarantar za ta ci gaba da aiki kamar yadda aka tsara,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa a halin yanzu ɗaliban yankin na samun karatu a wasu makarantu masu isassun kayayyakin more rayuwa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata