DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, May 16, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tinubu da Bankin Duniya na tattaunawa kan sabon bashin Dala biliyan...

Gwamnatin Tinubu da Bankin Duniya na tattaunawa kan sabon bashin Dala biliyan 1.25

Gwamnatin Nijeriya ta ƙara ƙaimi wajen tattaunawa da Bankin Duniya domin samun sabon bashin dala biliyan 1.25 saboda tallafa wa gyaran tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa gasa a kasuwanci.

Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa bashin, wanda aka sanya wa suna Nigeria Actions for Investment and Jobs Acceleration, ya kai wani muhimmin mataki a tsarin amincewar Bankin Duniyar, inda ake sa ran za a gabatar da shi domin amincewa a ranar 26 ga Yunin 2026.

Wannan sabon bashin zai zama na biyu mafi girma da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu daga Bankin Duniya, bayan bashin dala biliyan 1.5 da aka amince da shi a watan Yunin 2024 domin daƙile matsalolin tattalin arziki da bunƙasa ci gaba.

Idan aka yi la’akari da canjin kuɗi na naira 1,361.4 kan dala ɗaya, bashin na dala biliyan 1.25 zai kai kimanin naira tiriliyan 1.70, lamarin da ke nuna yadda gwamnati ke ci gaba da neman tallafin kuɗaɗe daga ƙasashen waje yayin aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki.

Rahoton ya ƙara da cewa idan aka amince da bashin kuma aka fitar da kuɗin gaba ɗaya ba tare da jinkiri ba, bashin waje na Najeriya zai tashi daga naira tiriliyan 74.43, wato dala biliyan 51.86 zuwa akalla naira tiriliyan 76.13, daidai da dala biliyan 53.11.

Haka kuma jimillar bashin gwamnatin Najeriya zai ƙaru daga naira tiriliyan 159.28 zuwa akalla naira tiriliyan 160.98, yayin da a ma’aunin dala zai iya ƙaruwa daga dala biliyan 110.97 zuwa kusan dala biliyan 112.22 idan aka kammala yarjejeniyar.

Takardun bayanan shirin da Bankin Duniya ya wallafa sun nuna cewa an wuce matakan farko na nazari da tantancewa, inda aikin yanzu ya kai matakin yanke hukunci, wanda shugabannin bankin ke duba bayanan ƙarshe kafin kaiwa kwamitin gudanarwa domin amincewa ta ƙarshe.

Takardar ta nuna cewa an riga an cimma matsaya kan muhimman manufofi, sharudan bayar da bashin da kuma sauye-sauyen da gwamnatin Najeriya ta amince za ta aiwatar.

Bankin Duniyan ya bayyana cewa an tsara bashin ne domin taimaka wa gwamnati wajen faɗaɗa samun kuɗaɗen tallafi, bunƙasa harkokin dijital da wutar lantarki, tare da ƙarfafa gasa ta hanyar sauye-sauye a haraji, kasuwanci da harkar noma.

Rahoton ya kuma nuna cewa yawan dogaro da gwamnatin Tinubu ke yi da bashin cibiyoyin ƙasa da ƙasa na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce, inda bincike ya nuna cewa Bankin Duniya ya amince da bashi da tallafin kuɗi na kusan dala biliyan 9.35 ga Najeriya tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Mayun 2026.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata