DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jam’iyyar PDP a jihar Zamfara ta caccaki karamin ministan tsaro, Bello Matawalle bisa goyon bayan dakatar da gwamnan jihar Rivers

-

Bello Matawalle

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wani jawabi da ya yi a ranar Talata ya kafa dokar ta baci a jihar Rivers tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida sakamakon rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar. 

Shugaban ya kuma nada Vice Admiral Ibok-Ette Ibas mai ritaya, a matsayin mai kula da harkokin mulki na jihar na rikon kwarya.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro ya fitar a ranar Talata, ya ce matakin da shugaban kasar ya dauka na da matukar muhimmanci wajen maido da kwanciyar hankali a fagen siyasar jihar.

Ministan ya bayyana cewa sanya dokar ta bacin shine abinda da ya dace don magance rikicin siyasa da ke ci gaba da ruruwa a jihar, wanda ya samu cikas wajen gudanar da mulkin dimokradiyya da kuma jin dadin al’ummar jihar Rivers.

Sai dai shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara Jibo Magayaki Jamilu a wata sanarwa da ya fitar jiya ya ce goyon bayan da Bello Matawalle ya bayar kan dakatarwar da aka yi wa Gwamna Siminalayi Fubara ba bisa ka’ida ba ba abin mamaki ba ne, idan aka yi la’akari da irin tarihin da ya yi na tauye ka’idojin dimokaradiyya da ‘yancin dan Adam a lokacin da yake Gwamnan Jihar Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rukunin farko na maniyyatan jihar Bauchi a Nijeriya, sun tashi zuwa Saudiyya- NAHCON

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya ta bayyana cewa maniyyata 2,520 ne daga cikin jihar Bauchi za su halarci aikin Hajjin bana na 2025 a kasar...

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su...

Mafi Shahara