DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumomin mulkin sojan Nijar sun kama wasu ‘yan jarida uku na Radio Sahara da ke jihar Agadez

-

Rahotanni daga gidan Radio Sahara Fm da ke jihar Agadez sun tabbatar da kama wasu ‘yan jaridar gidan radiyon guda uku da suka hada da Hamid Mahmoud tsohon wakilin Muryar Amurka (VOA), da Maman Bachir Sani da kuma Masaouda Jaharou Sanda

Malan Anisse daya daya daga cikin shugabannin kafar ya shaida wa DCL cewa tun ranar Alhamis ne aka kama abokan aikin nasu, kuma har yanzu haka ana cigaba da tsare su a ofishin hukumar ‘yan sanda na jihar kafin a gabatar da su a gaban alkali.

Google search engine

An kama wadannan ‘yan jaridar ne dai sakamakon zargin su da bada labarin da ba gaskiya ba, kan cewa hukumomin kasar Nijar sun yanke hulda da hukumomin Rasha da na Turkiyya wanda suka ce su ma sun same shi ne daga wata kafa ta ketare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mutanen kauyen da suka sayar da buhunan masara don hada N40m suka biya kudin fansa, aka karbi kudin aka kuma ki sako mutanen a...

Dattawan al’ummar Gidan Waya da ke ƙaramar hukumar Lere a jihar Kaduna sun bayyana cewa sun sayar da buhunan masara sama da 3,000 domin tara...

Sojoji sun amince an kitsa yunkurin juyin mulki kan Tinubu

Rundunar sojin Najeriya ta amince cewa wasu jami’anta sun kitsa yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne...

Mafi Shahara