Tuesday, April 7, 2026
HomeUncategorizedMalaman jami'ar jihar Kaduna (KASU) sun tsunduma yajin aiki

Malaman jami’ar jihar Kaduna (KASU) sun tsunduma yajin aiki

 

Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, reshen jami’ar Kaduna, KASU, ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 18 ga watan Fabrairu.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Dakta Peter Adamu da sakatarenta, Dokta Peter Waziri, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya rawaito.

Sanarwar ta ce matakin ya biyo bayan amincewar majalisar zartaswar kungiyar ta kasa. 

Kungiyar ta bayyana daga cikin dalilan shiga yajin aikin da suka haɗa da rashin ingata walwalar ma’aikata da rike musu albashi, wanda ya hada da kashi 60 cikin 100 na albashin watan Satumban 2017 da kuma Mayu zuwa Satumban 2022.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata