DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeUncategorizedGwamnatin jihar Kano, za ta yi amfani da shawarwarin kwamitin bincike kan...

Gwamnatin jihar Kano, za ta yi amfani da shawarwarin kwamitin bincike kan zanga-zangar tsadar rayuwa

 

Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature D/Tofa, ya fitar ranar Talata.

Gwamnan ya yi alkawarin ne a lokacin lokacin da ya karbi rahoto daga shugaban kwamitin da aka kafa da daya gudanar da bincike kan zanga zangar da aka gudanar a ranar 1 ga Agusta, 2024, bisa jagorancin mai shari’a Lawan Wada (mai ritaya), yayin taron majalisar zartarwa ta jihar Kano daya gudana a gidan gwamnati ranar Talata.

Rahoton kwamitin ya ce akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu bakwai suka samu munanan raunuka a jihar Kano.

A cewar rahoton an kuma lalata kadarorin gwamnati da daidaikun mutane da suka haura N11bn a lokacin zanga zangar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata