Gwamnatin kasar Indonesia ta dakatar da lasisin manhajar TikTok biyo bayan kin ba da bayanan zanga-zangar kin gwamnati kamar yadda ma’aikatar yada labarai da harkokin zamani ta bayyana a ranar Juma’a.
Ma’aikatar ta bayyana cewa ta dakatar da lasisin manhajar TikTok na wucin-gadi saboda gaza samar da cikakken bayani kan ayyukan masu zanga-zangar adawa da gwamnati da aka gudanar a watan Agusta.
A cikin sanarwar, Darakta Janar na kula da kafofin sadarwar zamani, Alexander Sabar, ya ce, wannan mataki na daga cikin nuna ƙarfi da ƙudurin gwamnati bayan rashin samar da bayanai wadatattu da TikTok din ta yi.
