Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ce kasuwar Jilli da ke karamar hukumar Gubio — inda aka kai harin sama da ya yi sanadin mutuwar fararen hula — an rufe ta tun shekaru biyar da suka gabata.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Malam Dauda Iliya ya fitar, ya ce gwamnan ya bayyana cewa kasuwar ta zama wurin da ake zargin masu aikata laifuka da masu taimaka musu ke amfani da ita.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnan ya ce ya samu cikakken bayani kan harin saman da rundunar Operation Hadin Kai ta kai a yankin, wanda ke kan iyakar jihohin Borno da Yobe.
Zulum ya kara da cewa gwamnatin Borno na tuntubar gwamnatin Jihar Yobe da manyan hafsoshin soji domin fahimtar abin da ya faru da daukar mataki.
