Sa’o’i kaɗan bayan gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewa daga takarar neman wa’adi na biyu, wani mutum mai suna iri ɗaya da na shi ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan jihar a zaɓen shekarar 2027.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa mutumin mai suna Blessing Fubara ta sayi fom ɗin neman takara da nuna sha’awa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) domin tsayawa takarar gwamnan jihar Rivers.
Rahoton ya ce Blessing Fubara ya karɓi fom ɗin nasa ne a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja ranar Laraba, inda lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu bibiyar siyasar jihar Rivers.
An bayyana Blessing Fubara a matsayin masani kan harkokin al’umma gyaran birane, wanda ya taɓa aiki a fannoni daban-daban na bayar da shawarwari ga hukumomin gwamnati da shirye-shiryen tallafa wa matasa.
Ko da yake shi da Gwamna Siminalayi Fubara duk sun fito ne daga ƙaramar hukumar Opobo/Nkoro ta jihar Rivers, har yanzu babu tabbacin ko suna da alaƙar jini ko dangantaka ta kusa.
Shugaban jam’iyyar NDC a jihar Rivers, Hon. Success Jack, ya tabbatar da cewa Blessing Fubara na daga cikin masu neman takarar gwamna a jam’iyyar, sai dai ya ce shi ma bai san ko yana da alaƙa da gwamnan jihar ba.
A cewarsa, jam’iyyar NDC na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, inda ta ke da burin lashe sauran muƙaman siyasa a jihar Rivers.
Rahoton ya kuma bayyana cewa Blessing Fubara ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa NDC kimanin makonni biyu da suka gabata, inda aka tarbe shi tare da wasu magoya bayansa a Abuja.
Yayin sauya shekar tasa, ya bayyana cewa ya shiga jam’iyyar NDC ne domin kare muradun al’ummar jihar Rivers, yana mai cewa jihar na buƙatar sabon salo na siyasa da shugabanci kafin zaɓen 2027.
Bayyanar Blessing Fubara a takarar gwamna ta haifar da martani daban-daban a siyasar jihar Rivers, inda wasu magoya bayan NDC ke kallon sa a matsayin sabon jigo da zai kawo sauyi, yayin da masu suka ke ganin babban ƙalubalen sa shi ne yadda zai gina karɓuwa da ƙarfi a faɗin jihar domin gogayya da manyan jam’iyyun siyasa.
