Madugun adawa a Nijeriya Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Tinubu kan kalaman da ya yi na kwatanta farashin mai a Nijeriya da na wasu kasashen Afirka, yana mai cewa hakan bai nuna hakikanin halin da ‘yan Nijeriya ke ciki ba.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a Abuja , Atiku Abubakar ya ce maganar shugaban kasar ta zo ne bayan ziyararsa zuwa jihar Bayelsa, inda ya bukaci ‘yan Nijeriya su gode cewa farashin mai a kasar ya fi na kasashe kamar Kenya sauki, duk da wahalhalun da ake ciki.
A cewarsa, duk da cewa farashin mai a Nijeriya na iya rashin tsada da na wasu kasashe, rayuwa a kasar ta fi tsada idan aka duba yadda kudin shiga ke raguwa da kuma hauhawar farashi.
