Dan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar NDC Peter Obi, ya ce ba zai janye wa ɗan takarar ADC Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.
Obi ya ce duk wata shawara da za a yanke kan yiwuwar haɗa kan jam’iyyun adawa, ya kamata ta fito daga jam’iyyun siyasa, ba daga ’yan takarar kansu ba.
Ya ce batun ba ya kan ko shi ko Atiku zai janye wa ɗayan, domin a yanzu kowannensu ɗan takarar shugaban ƙasa ne a wata jam’iyya daban, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise, inda ya yi magana kan zaɓen 2027, haɗin kan ’yan adawa, tattalin arziki, haɗin kan ƙasa, tsaro da shugabanci.
Wannan furucin na Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin haɗa kan ’yan siyasar adawa domin samar da wata kafa guda da za ta iya ƙalubalantar shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A shekarar 2025, Obi, Atiku da wasu jagororin adawa sun shiga ƙungiyar haɗin kan ’yan adawa wadda ta zaɓi ADC a matsayin dandalinta na siyasa. Hakan ya haifar da tsammanin cewa tsoffin abokan hulɗar za su sake yin aiki tare gabanin zaɓen 2027.
Sai dai haɗin kan bai kai ga Obi da Atiku sun tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyya ɗaya ba.
Daga bisani Obi ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, yayin da Atiku ya zama ɗan takarar ADC.
Tun daga lokacin, kasancewar ’yan takarar biyu a jam’iyyu daban-daban ya ƙara haifar da hasashen ko ɗayansu zai iya janye wa ɗayan domin samar da ɗan takara guda da zai wakilci ’yan adawa a zaɓen 2027.
