Tawagar tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ta bayyana cewa, babu wani shugaban ƙasa mai ci da aka taɓa kayarwa daga ɗan takarar adawa da ya fito daga yankin siyasa ɗaya da shi.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jigon tafiyar Atiku, Olusola Sanni ya fitar, inda ya soki masu neman ci gaba da bai wa kudancin Najeriya mulki a ƙarƙashin tsarin karɓa-karɓa tsakanin arewa da kudu.
Sanni ya ce zuwa shekarar 2027, kudancin Najeriya zai kasance ya yi kusan shekara 18 yana mulkin ƙasa a jamhuriya ta huɗu, yayin da arewa ta yi shekaru 10 kacal.
Ya ƙara da cewa idan aka bai wa kudu damar ci gaba da mulki na wasu shekaru huɗu, tazarar za ta ƙara faɗaɗa.
Olusola Sanni ya ce saboda haka abu ne mai wuya a fahimci adalcin hujjar da ke neman ƙara faɗaɗa rashin daidaito da ake da shi a yanzu da sunan daidaito.
Sanarwar ta kuma zargi wasu ‘yan siyasa da nuna son kai a batun tsarin karɓa-karɓa, musamman waɗanda suka goyi bayan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a shekarar 2011, bayan rasuwar marigayi Umaru Musa Yar’Adua.
Sai dai bangaren Atikun ya amince cewa yankin Kudu maso Gabas na da burin samar da shugaban ƙasa, amma tare gargadi ga masu ruwa da tsaki da kada a mayar da wannan buƙata tamkar cinikin siyasa kawai domin biyan bukatar mutum ɗaya.
Bangaren tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya a buƙaci jam’iyyun adawa su mayar da hankali wajen gina haɗakar ƙasa baki ɗaya domin kayar da gwamnatin da ke mulki.
