Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuBabu wani jami'in gwamnatin jihar Plateau da ya zo yi mana ta'aziyyar...

Babu wani jami’in gwamnatin jihar Plateau da ya zo yi mana ta’aziyyar mutanenmu da aka yi ajalinsu – Sarkin Zazzau

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Amb Ahmed Nuhu Bamalli, ya nuna damuwarsa kan yadda babu wata tawagar jami’an gwamnati daga Jihar Plateau da ta zo Zaria domin yi wa iyalan waɗanda aka kashe a ƙaramar hukumar Mangu na jihar ta’aziyya.

An dai kashe mutanen ne a hanyar su ta zuwa ɗaurin aure daga jihar ta Plateau daga jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda aka kai hari kan wasu matafiya su 31 da ke hanyarsu zuwa ɗaurin aure, inda wasu 13 suka rasa rayukansu, yayin da wasu suka jikkata, sannan aka ƙone motar da suke ciki kurmus.

Mai Martaba Sarkin ya bayyana haka ne yayin da yake karɓar tawagar shugabannin addinai ƙarƙashin jagorancin tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, a fadarsa da ke Zaria jihar Kaduna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata