Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, Shehu Buba, ya musanta zarge-zargen da ake yi masa na alaƙa da ‘yan bindiga, yana mai bayyana bidiyoyi da bayanan da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta a matsayin ƙoƙarin ɓata masa suna.
Buba, wanda tsohon shugaban kwamitin majalisar dattawa ne kan tsaron ƙasa da leken asiri, ya ce zarge-zargen sun fara ne tun shekarar 2024, bayan da ya kai ziyara ga iyalan wasu mutane da aka hallaka.
A cewar sa ya yi Allah-wadai da kisan tare da neman hukumomi su tabbatar da an yi adalci ga iyalan mamatan.
Jaridar Punch ta ruwaito ya ce sabon zargin ya biyo bayan wasu bidiyoyi da wani matashi mai amfani da kafafen sadarwa mai suna ‘D English Alhaji’ ya yaɗa, inda aka yi ikirarin cewa wasu jagororin ‘yan bindiga sun ziyarci gidansa.
Sai dai sanatan ya ce zargin ba shi da tushe, domin bidiyon ya haɗa wasu hotuna da faifan bidiyo daban-daban.
A cewarsa, ɗaya daga cikin faifan bidiyon na nuna mahajjatan Kaduna da suka ziyarci gidansa a shekarar 2023, yayin da ɗayan ke nuna wasu mutane daban.
Ya kuma ce amfani da waɗannan bidiyoyi a matsayin hujjar cewa ‘yan bindiga sun ziyarci gidansa ba daidai ba ne.
Buba ya kara da cewa wani matashi mai suna Hassan Husseini, wanda ya taɓa taimaka masa wajen samun ilimi ne ya ɗauki wasu hotuna da bidiyoyin mutanen da ke ziyartar gidansa.
Ya yi zargin cewa daga baya aka yi amfani da waɗannan bayanan wajen yaɗa zarge-zargen da suka shafe shi.
Sanatan ya ce ya kai ƙara ga rundunar ‘yan sandan Nijeriya a watan Satumbar 2025, bayan da wasu daga cikin masu yaɗa bidiyoyin suka nemi kuɗi daga gare shi.
Ya ce an kama wasu mutane kuma an gurfanar da biyar daga cikinsu a gaban kotu, inda ake ci gaba da shari’ar.
Buba, wanda ke neman takarar gwamnan Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar PRP, ya ce a shirye yake a binciki ayyukansa, amma ya kamata irin wannan bincike ya dogara da sahihan hujjoji.
Ya yi kira ga ‘yan jarida da masu tantance bayanai su rika bincikar zarge-zarge kafin yaɗa su, yana mai cewa siyasar adawa bai kamata ta zama hanyar ɓata suna ba.
