DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, September 13, 2026
HomeLabaraiDangote ya rage N100 a kudin man jirgin sama

Dangote ya rage N100 a kudin man jirgin sama

Matatar Dangote ta sanar da rage farashin man jiragen sama wato Jet A1 daga N1,750 zuwa N1,650 kan kowace lita, domin rage wa kamfanonin jiragen sama radadin tsadar aiki tare da tabbatar da wadatar man fetur a Nijeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa matakin na daga cikin kokarin da matatar ke yi na tallafawa harkokin sufurin jiragen sama a Nijeriya.

Rahoton ya bayyana cewa wannan sabon ragin farashi zai taimaka wajen rage yawan kudaden da kamfanonin jiragen sama ke kashewa wajen gudanar da ayyukansu, musamman ganin cewa man jirgi na daga cikin manyan abubuwan da ke kara tsadar zirga-zirgar jirage.

A baya-bayan nan dai wasu kamfanonin jiragen sama a Nijeriya sun rage yawan tafiye-tafiyensu saboda tashin gwauron zabi da farashin man jirgi ya yi, inda a wasu lokutan farashin ya haura N2,500 kan kowace lita.

Kungiyar masu kamfanonin jiragen sama ta Nijeriya AON ta taba yin barazanar dakatar da zirga-zirgar jirage saboda matsin tattalin arzikin da suke fuskanta sakamakon tsadar man jirgi.

Sai dai bayan shiga tsakani da gwamnatin Nijeriya ta yi tare da gudanar da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki, kamfanonin sun janye barazanar, duk da cewa har yanzu suna kokawa kan tsadar gudanar da aiki.

Matatar Dangote ta kuma bayyana cewa baya ga rage farashin, ta samar da damar bashi na kwanaki 30 ba tare da ruwa ba ga dillalan mai da masu kamfanonin jiragen sama.

Haka kuma kamfanin ya sauya tsarin sayar da man daga amfani da dalar Amurka zuwa tsarin naira, matakin da ake ganin zai taimaka wajen rage matsin canjin kudade ga masu harkar jiragen sama.

Matatar Dangote ta ce wadannan matakai za su taimaka wajen rage kudin sayen mai, inganta gudanar da ayyukan jiragen sama da kuma rage farashin tikitin tafiye-tafiye a Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata