Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedGwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan kasuwa da su rage farashin kayan abinci

Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan kasuwa da su rage farashin kayan abinci

 

Ministan Noma da albarkatun kasa Abubakar Kyari ne ya bayyana bukatar hakan a ranar Talata, a yayin wani bikin noman alkama da aka gudanar a kauyen Dabi dake karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.

Ministan ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu ‘yan kasuwa suka ki sauke farashi duk da saukowar kayayyaki, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin kishin ƙasa.

Ya ce gwamnatin tarayya tana sane da saukar farashin kayan abinci a wasu manyan kasuwanni, musamman na kayan masarufi kamar su gari, sukari, shinkafa da taliya.

Amma duk da haka wasu, masu yin burodi, da masu shaguna a cikin Unguwanni sun ki sauke farashin kayyayyakin amfanin yau da kullum, a saboda haka ya yi kira da su sauke farashi kamar yadda yake sauka a wasu kasuwanni.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata