Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce samar da isassun kuɗaɗe na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro da gudanar da babban zaɓen 2027 cikin nasara.
Amupitan ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da saƙon fatan alheri a wajen taron horaswa na shida da aka shirya wa manyan jami’an ƴan sanda a Owerri.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Shugaban INEC, Adedayo Oketola, ya fitar ranar Laraba, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
An gudanar da taron ne ƙarƙashin taken, “Ƙirƙirar taswirar ‘yan sandan Nijeriya domin gudanar da tsaro yayin zaɓe,” inda aka fi mayar da hankali kan tsaron zaɓe.
Shugaban INEC ya ce ana buƙatar ci gaba da samar da kuɗaɗe domin tabbatar da samar da tsaro da kayan aikin da ake buƙata wajen gudanar da zaɓe yadda ya kamata a faɗin ƙasar.
Ya ce kundin tsarin mulki ya tanadi kuɗaɗen INEC a matsayin abin da ake bai wa fifiko wajen cire kuɗi daga Asusun Kuɗaɗen Shiga na Ƙasa.
Sai dai Amupitan ya ce yawan nauyin da ke kan hukumar na buƙatar ci gaba da samun tallafin kuɗi domin ta iya sauke nauyin da kundin tsarin mulki da dokoki suka ɗora mata yadda ya kamata.
Ya ce INEC ce ke gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa, gwamnoni da ’yan Majalisun Dokokin Jihohi a faɗin ƙasar.
Ya ƙara da cewa hukumar ce ke da alhakin rajistar masu kaɗa ƙuri’a da kuma rajistar jam’iyyun siyasa.
Amupitan ya ce ikon da doka ta bai wa INEC na neman tura jami’an tsaro domin gudanar da zaɓe da rajistar masu kaɗa ƙuri’a ya sa tsaro ya zama wani muhimmin ɓangare na tsarin zaɓe.
Ya ce, “Wani lokaci, ba abin da mutum yake son yi ne zai iya yi ba, saboda ƙarancin kuɗi.”
Ya bayyana cewa hukumomin gwamnati, ciki har da ’yan sanda da INEC, dole ne su gudanar da ayyukansu bisa kuɗaɗen da aka ware musu da kuma kasafin kuɗin da aka amince da shi.
Shugaban INEC ya jaddada cewa rajistar masu kaɗa ƙuri’a ita ce ginshiƙin ingantaccen zaɓe, yana mai gargadin cewa rajistar da ke ɗauke da bayanan da ba daidai ba ko kuma waɗanda suka tsufa na iya kawo cikas ga damar kowa ta shiga zaɓe.
Ya ce ya kamata a ɗauki kuɗaɗen gudanar da zaɓe, ciki har da na tsaro, a matsayin nauyin ƙasa baki ɗaya, saboda INEC ce ke gudanar da zaɓe a matakai uku na gwamnati a Nijeriya.
Amupitan ya ce isasshen kuɗi na da matuƙar muhimmanci wajen tura jami’ai da kayan zaɓe zuwa ƙananan hukumomi, mazabu, wuraren rajista da rumfunan zaɓe.
Ya ce rashin isassun kayan aiki da hanyoyin sufuri na iya kawo cikas ga zaɓe, ko da kuwa hukumomin tsaro sun yi nasarar tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da zaɓen.
Shugaban INEC ya ce tsaro da kayan aiki sun zama abubuwan da suka fi bai wa hukumar muhimmanci a ƙarƙashin jagorancinsa, yana mai cewa INEC na aiki tare da gwamnati da hukumomin tsaro gabanin zaɓen 2027.
