Ministan Abuja Nyesom Wike, ya ce suna shirya wata sabuwar dabarar siyasa da za ta dakile nasasar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, a zaɓen 2027.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Wike ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake magana da manema labarai bayan duba wasu ayyukan gine-gine a birnin.
Ya kuma fayyace cewa dabarar ƙungiyar G5 a zaɓen 2023 ta fi karkata ne wajen rage kuri’un Atiku a yankin Kudu maso Kudu, ba wai Peter Obi ba.
A cewarsa, G5 ta ƙarfafa masu zaɓe a yankin da su zaɓi Obi domin hana Atiku samun isassun kuri’u, duk da cewa PDP ce ke da ƙarfi a yankin.
Wike ya ce da al’ummar Kudu maso Kudu sun zaɓi Atiku gaba ɗaya bisa tsarin jam’iyya, da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya samu damar lashe zaɓen.
Game da zargin magudin zaɓe a Rivers, Wike ya ce ba bu wata hujja mai ƙarfi a gaban kotun zaɓe da ke nuna cewa Labour Party ta lashe jihar ba.
Ya ƙara da cewa kowace ƙungiyar siyasa na da dabarunta a zaɓe, amma ba lallai ta bayyana su tun kafin lokacin ba, yana mai cewa za a yi amfani da dabarun da suka dace wajen kare muradun siyasa a 2027.
