DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeKetareKasashen kungiyar AES sun fice daga kotun ICC

Kasashen kungiyar AES sun fice daga kotun ICC

 

Kasashen kungiyar AES sun ayyana ficewarsu daga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa wato ICC.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar, kuma shugaban kasar Mali, ya rattaba wa hannu a ranar 22 ga watan Satumba, kasashen uku na yankin Sahel da ke karkashin mulkin soja sun bayyana hakan bayan wasu zarge-zarge da suka yi wa kotun.

Daga cikin zarge-zargen da kasashen suka yi har da ikirarin cewa kotun ta kasa gurfanar da wasu da suka kira shafaffu da mai ne, wadanda suka fi karfin doka duk kuwa da laifukan da ake zarginsu da aikatawa.

Haka kuma, kasashen sun zargi kotun da zama ’yar amshin shatar wasu kasashen turawan mulkin mallaka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata