Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce tsaro da sauran ayyukan jin kai sun cinye kusan kashi 70 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar a cikin shekaru bakwai da suka gabata.
Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin taron kwamitin gudanarwa karo na huɗu na shirin Majalisar Ɗinkin Duniya mai suna UN Offer Support to the Borno Model, da kuma taron kwamitin gudanarwa na ayyukan asusun gina zaman lafiya na majalisar ɗinkin duniya, da aka gudanar a Maiduguri.
A cewar gwamnan, yawan kuɗaɗen da aka kashe ya samo asali ne sakamakon matsalar Boko Haram, wadda ta haifar da ɗimbin buƙatun tsaro da na jin kai a jihar.
Ya ce kuɗaɗen sun shafi tallafawa ’yan gudun hijira, ’yan gudun hijira da suka dawo, sake gina gidaje da sauran ababen more rayuwa, da samar da hanyoyin samun abin dogaro da kai ga mutanen da rikicin ya shafa.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta zuba jari mai yawa wajen sake gina makarantu, gidaje, cibiyoyin lafiya da kasuwanni, tare da samar da sana’o’i da hanyoyin dogaro da kai ga al’ummomin da rikicin ya shafa.
Zulum ya kuma yaba wa hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin bayar da tallafi bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen taimakawa jihar wajen sauya daga ayyukan agajin gaggawa zuwa farfaɗowa, sake ginawa da samar da ci gaba mai ɗorewa.
Ya bukaci abokan hulɗar ci gaba da su daina dogaro da ƙananan ayyukan agaji na ɗan lokaci kawai, su mayar da hankali kan shirye-shiryen dogon lokaci da za su haɗa gina zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziki.
Gwamnan ya jaddada cewa ba za a iya samun zaman lafiya mai ɗorewa ba tare da samar da ayyukan yi, ilimi, hanyoyin samun abin dogaro da kai, ingantattun hukumomi da dama ga matasa ba.
A nasa jawabin, Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare, Sanata Abubakar Bagudu, ya ce matsalolin jin kai da ci gaban da Nijeriya ke fuskanta na buƙatar ci gaba da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.
Ya ce ya zama dole a fara sauya tallafin gaggawa zuwa zuba jari na dogon lokaci, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, bunƙasa ƙwarewar ɗan Adam, jure sauyin yanayi da haɓaka tattalin arziki.
Taron ya samu halartar jami’an gwamnati, hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya, jami’an tsaro, ƙungiyoyin jin kai, abokan hulɗar ci gaba da wakilan ƙasashe masu bayar da tallafi.
