DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 14, 2026
HomeLabaraiKotu ta sanya Naira miliyan 200, a matsayin kuɗin belin El-Rufa'i

Kotu ta sanya Naira miliyan 200, a matsayin kuɗin belin El-Rufa’i

Babbar kotun Nijeriya da ke zamanta a Kaduna ta bayar da beli ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin cin hanci da rashawa da Hukumar Yaki da Cin Hanci da sauran Laifuffuka ICPC ta shigar a kansa.

Alkalin kotun, Rilwanu Aikawa, ya yanke hukuncin ne bayan sauraron hujjojin bangarorin biyu, inda ya amince da bayar da belin naira miliyan 200 tare da mutane biyu da za su tsaya masa, yana mai bayyana sharuddan a matsayin masu tsauri.

Sai dai kotun ta umurci cewa El-Rufai zai ci gaba da zama a hannun ICPC har sai ya cika dukkan sharuddan belin, ciki har da gabatar da masu tsaya masa da kuma cika bukatun da aka gindaya.

Daga cikin sharuddan, dole ne daya daga cikin masu tsaya masa ya kasance ma’aikacin gwamnati daga mataki na 15 zuwa sama, yayin da dayan kuma dole ne ya zama sarki ko shugaba na gargajiya da aka amince da shi, tare da ajiye fasfo dinsu a kotu.

Har ila yau, kotun ta hana El-Rufai yin duk wani bayani ga jama’a dangane da shari’ar, tare da umurtarsa da ya rika halartar duk zaman kotu ba tare da gazawa ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Lamarin na zuwa ne yayin da tsohon gwamnan ke fuskantar shari’o’i daban-daban a kotuna, lamarin da ke kara janyo hankali kan batun yaki da rashawa a Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata