Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedRashin tsaro da tashe-tashen hankula sun ragu da kashi 90% a Nijeriya...

Rashin tsaro da tashe-tashen hankula sun ragu da kashi 90% a Nijeriya – Ribadu

Nuhu Ribadu

Mai bai awa shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya bayyana cewa Nijeriya ta samu ci gaba sama da kashi 90 cikin 100 akan rashin tsaro a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Ribadu ya bayyana haka ne a garin Jos na jihar Filato a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da kwamandan rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Janar Folusho Oyinlola a ofishinsa, biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai kan al’ummar Bokkos wanda ya yi sanadin mutuwar mazauna garin.

A cewarsa, gwamnatin shugaba Tinubu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.

Ya ce cikin shekaru 2 da suka wuce, an samu ragin yawan mace-mace da  tashin hankali da kusan kashi 90 cikin 100 a kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata