Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NDC, Sanata Kabiru Gaya, ya amince da komawa jam’iyyar APC, bayan wata ganawa da ya yi da shugaban jam’iyyar na Nijeriya, Farfesa Nentawe Yilwatda.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Sanata Gaya ya cimma wannan matsaya ne bayan wata ganawar sirri da ya yi da shugaban APC a gidansa da ke Abuja a daren ranar Litinin.
Majiyar da ke da masaniya kan ganawar ta bayyana cewa tattaunawar ta ɗauki kusan mintuna 45, kuma a ƙarshe Sanata Gaya ya amince da komawa jam’iyyar APC.
Wannan ci gaba ya biyo bayan rahotannin da suka ce Sanata Gaya ya rasa tikitin takarar sanatan Kano ta Kudu a jam’iyyar NDC, duk da cewa kwanan nan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar domin tunkarar zaɓen shekarar 2027.
Sanata Gaya ya bar APC ne a ranar 5 ga Afrilu, inda ya fara shiga jam’iyyar ADC, kafin daga bisani ya koma jam’iyyar NDC tare da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kabiru Gaya ya taba zama gwamnan jihar Kano tsakanin shekarun 1992 zuwa 1993 a lokacin jamhuriya ta uku.
Daga bisani ya wakilci mazabar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawan Nijeriya daga shekarar 2015 zuwa 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
A zaɓen shekarar 2023, Sanata Gaya ya sha kaye a hannun Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, wanda ya yi takara a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP.
