Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya roki kungiyar kwadago ta NLC da TUC da kada su tafi yajin aikin da suka kudurci aniya a makon gobe.
Kungiyar kwadagon dai ta ware ranar Talata 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta tsunduma yajin aiki na sai baba-ta-gani biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce akwai bukatar a kara ba gwamnatin tarayya dama, kada a yi gaggawar tsunduma yajin aiki.
Ya ce ya shiga cikin sulhu da tattaunawa daban-daban da kungiyar kwadago a lokutta daban-daban, inda ya gano cewa yajin aikin zai kara jefa kasa cikin mawuyacin hali

Gaskiya tafiya yajin aiki ba shine MAFITA ba.Illa dai hakan zai Kara jefa TALAKA CIKIN KUNCIN RAYUWA.