DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, September 24, 2026
HomeSiyasaTsofaffin ƴan majalisar dokoki sun goyi bayan sake zaben Tinubu a 2027

Tsofaffin ƴan majalisar dokoki sun goyi bayan sake zaben Tinubu a 2027

Tsofaffin shugabannin majalisun dokokin jihohin Nijeriya da wasu tsofaffin ’yan majalisar tarayya sun bayyana goyon bayansu ga sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027, tare da alkawarin kai manufofi da shirye-shiryen gwamnatinsa zuwa ga jama’a a matakin kasa.

Jaridar The Nation ta ruwaito kungiyar tsofaffin shugabannin majalisun dokokin jihohin Nijeriya (FOPSHAN) ta bayyana hakan ne a wani taro da ta gudanar a Abuja, inda ta amince da Tinubu domin wa’adi na biyu, tare da cewa za ta tura mambobinta zuwa jihohi 36 da Abuja domin wayar da kan jama’a kan manufofin gwamnatin.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim, wanda ya jagoranci taron, ya kare sauye-sauyen gwamnatin Tinubu, yana mai cewa wasu daga cikinsu an tsara su ne domin amfanin al’ummomi na yanzu da kuma masu zuwa.

Ya ambaci cire tallafin man fetur, tsarin rancen karatu da shirin kafa ’yan sandan jihohi a matsayin wasu daga cikin manufofin da ya ce za su iya samar da tasiri na dogon lokaci.

Tsohon gwamnan Plateau kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Sanata Simon Lalong, ya ce dole ne sauye-sauyen tattalin arziki su haifar da saukin rayuwa ga ’yan Nijeriya. Ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ya kara tsadar sufuri da rayuwa, don haka ya kamata gwamnati ta mayar da hankali kan abinci, noma, tsaro, ababen more rayuwa, samar da ayyukan yi da tallafa wa matasa.

Shi ma Gwamnan Ebonyi, Francis Ogbonna Nwifuru, ya bukaci tsofaffin ’yan majalisa da su ci gaba da taka rawa wajen ci gaban kasa, maimakon su zama masu kallo bayan barin mukaman siyasa. Ya ce gogewarsu na majalisa na da muhimmanci wajen inganta hadin gwiwa tsakanin bangaren zartarwa da majalisa da kuma karfafa tsarin dimokuraɗiyya.

A nata bangaren, uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, wadda ta halarci taron a matsayin babbar bako, ta gode wa tsofaffin ’yan majalisar kan goyon bayan da suka bayyana. Ta bukace su da su ci gaba da amfani da kwarewa da alaka da suka samu wajen hidimtawa kasa, tare da jagorantar matasa da taimakawa wajen karfafa dimokuraɗiyya da ci gaban al’ummominsu.

Shugaban FOPSHAN, Sanata Wasiu Eshilokun-Sani, ya ce taron ya kuma ba tsofaffin ’yan majalisar damar tattauna manyan manufofin gwamnati tare da duba kalubalen aiwatar da su.

Ya jaddada bukatar gaskiya, rikon amana da ingantaccen amfani da karin kudaden gwamnati, domin sauye-sauyen su haifar da ingantattun ayyukan jama’a da tasiri kai tsaye a rayuwar ’yan Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata