Kungiyar kwallon kafa a gasar Bundesliga ta kasar Jamus, Union Berlin, ta nada Marie-Louise Eta a matsayin koci wato mai horar da ‘yan wasa, lamarin da ya sa ta zama mace ta farko da ta taba zama babbar mai horar da ‘yan wasa a tarihin Bundesliga, bayan an sallami Steffen Baumgart a ranar Lahadi.
Eta ta zama mace ta farko da za ta horas da kungiyar maza a matakin koli a wata babbar gasar Turai. Ita mai shekaru 34, wadda ta taba zama mace ta farko a matsayin mataimakiyar koci a Bundesliga, za ta jagoranci kungiyar har zuwa karshen kakar wasa.
“Na yi matukar farin ciki da yadda kungiyar ta ba ni wannan aiki mai kalubale,” in ji Eta a cikin wata sanarwa.
An sallami Baumgart ne da safiyar Lahadi bayan rawar da kungiyar ta rika takawa ta yi rauni a kaso na biyu na kakar wasa, inda shan kaye da ci 3-1 a hannun Heidenheim da ke can kasan tebur a ranar Asabar ya zama sila ta karshe.
Union Berlin ta samu nasara sau biyu kacal tun bayan hutun Kirsimeti, kuma tana da maki bakwai ne kawai a saman gurbin wasan neman tsallake fadawa ajin dagaji.
“Mun yi rabin kakar wasa na biyu mai matukar takaici,” in ji daraktan wasanni Horst Held a cikin wata sanarwa.
“Halin da muke ciki har yanzu yana da hadari, kuma muna bukatar maki cikin gaggawa domin mu ci gaba da zama a gasar.
“Ayyukan da kungiyar ke yi a ‘yan makonnin nan ba su ba mu kwarin gwiwar cewa za mu iya juyar da al’amura da tsarin da muke ciki ba.”
A lokacin da take ‘yar wasa a Turbine Potsdam, Eta ta lashe gasar Champions League a shekarar 2010 tare da kofunan Bundesliga guda uku. Haka kuma ta riga ta amince cewa daga lokacin bazara za ta jagoranci kungiyar matan Union Berlin da ke Bundesliga.
