Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya musanta rahotannin da ke cewa yana neman zama Daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban Nijeriya Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Wike ya ce rahotannin ba su da tushe, yana mai cewa bai taɓa tattaunawa da kowa kan shugabanci ko kuma mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.
A cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman kan harkokin sadarwa da kafofin sada zumunta, Lere Olayinka, ya fitar ranar Litinin, Wike ya ce a halin yanzu ba ya Nijeriya ya tafi wata ƙasar domin hutawa bayan shafe sama da kwanaki 30 yana gudanar da ayyukan raya Abuja.
Ya ce a wannan lokacin ya halarci bikin ƙaddamar da ayyuka, ya aza harsashin wasu sabbin ayyuka tare da duba ayyukan da ake kan gudanarwa, musamman waɗanda ake shirin kammalawa da ƙaddamar da su a watan Disamba da Janairu na shekara mai zuwa.
Wike ya ce bayan dawowarsa Nijeriya, babban abin da zai fi mayar da hankali a kai shi ne ci gaba da gudanar da ayyukan da aka ɗora masa, tare da taimaka wa Shugaba Tinubu wajen samun nasara a siyasa.
Ya ce: “Idan na dawo, abin da za mu mayar da hankali a kai shi ne ci gaba da gudanar da ayyukan da aka ɗora mana bisa tsarin ajandar Renewed Hope na Shugaba Tinubu, tare da ƙara ƙarfafa damar samun nasarar zaɓensa a jihar Rivers da Abuja.”
Ministan ya kuma bayyana cewa ba sai ya samu wani matsayi a kwamitin yaƙin neman zaɓen kafin ya taimaka wajen ganin Tinubu ya sake lashe zaɓen 2027.
A cewarsa, “Ba na bukatar zama Darakta- ko ma mamba a kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban kasa na jam’iyyar APC domin bayar da tawa gudummawa wajen ganin ya samu gagarumar nasara a jihar Rivers da Abuja.”
Wike ya sake jaddada goyon bayansa ga ƙoƙarin Shugaba Tinubu na neman wa’adi na biyu, yana mai cewa zai yi aiki domin ganin Shugaban ya samu gagarumar nasara a jihar Rivers da Abuja a zaɓen 2027.
Ya ce duk da cewa ba ya neman wani matsayi a kwamitin yaƙin neman zaɓen, zai ci gaba da amfani da tasirinsa wajen tallafa wa nasarar siyasar Shugaba Tinubu.
