Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ’yan Nijeriya da su sake ba gwamnatinsa wata sabuwar damar domin ta samu damar kammala shirye-shirye da sauye-sauyen fasalin tattalin arziƙi da ta fara aiwatarwa a ƙasar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Tinubu ya yi wannan roƙon ne a ranar Juma’a yayin wani taron addu’ar Juma’a na musamman da aka gudanar a babban masallacin ƙasa da ke Abuja, a matsayin wani ɓangare na bikin cikar Nijeriya shekaru 66 da samun ‘yancin kai.
Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, wanda ya wakilci shugaban ƙasar a wurin taron, ya bayyana cewa gwamnatin yanzu tana aiki ne wajen gyara kura-kurai da kuma damammakin da gwamnatocin baya suka yi asararsu.
Da yake isar da saƙon shugaban ƙasa, Abbas ya buƙaci ‘yan Nijeriya da kada su cire rai game da farfaɗowar tattalin arziƙin ƙasar da ci gabanta.
Abbas ya ce, “Wannan zagayowar ranar, wato cika shekaru 66, tana nuna cewa Nijeriya ta balaga. Mutumin da ya kai shekara 66 ba za a ƙara kiransa yaro ba. Nijeriya ta zama ƙasa mai girma, koda yake idan muka kalli tafiyar daga samun ‘yancin kai zuwa yau, za mu iya cewa tafiya ce mai abubuwa daban-daban masu daɗi da akasinsu.”
Ya ƙara da cewa, “Saƙona ga ƙasa a madadin Shugaban Ƙasa, Shugaban Majalisar Dattawa, da dukkan mambobin Majalisar Ƙasa shi ne cewa kada ‘yan ƙasa su yanke ƙauna. Zaman lafiya na dawowa a wannan ƙasa. Ci gaba na dawowa a wannan ƙasa. Al’amura za su yi kyau yayin da muke ci gaba da tafiya a wannan dimokuraɗiyya.”
Tinubu ya jaddada cewa Nijeriya na kan turba madaidaiciya, inda ya ce ‘yan ƙasa sun gama yin sadaukarwa domin ƙasar ta sake zama babba.
“Ya kamata mu ba wannan gwamnatin ƙarin dama domin ta kammala kyakkyawan aikin da ta fara,” in ji shi.
Gwamnatin tarayya na gudanar da bukukuwan zagayowar ranar samun ‘yancin kai karo na 66 cikin sauƙi ba tare da kashe maƙudan kuɗaɗe ba, inda ta tsara jerin addu’o’in addini da taruka kafin ranar 1 ga Oktoba.
