DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, September 25, 2026
HomeLabaraiAmnesty ta yi Allah-wadai da kama masu sukar gwamnatin Kano

Amnesty ta yi Allah-wadai da kama masu sukar gwamnatin Kano

Kungiyar Amnesty International ta yi kakkausar suka kan yadda ake kara tauye ’yancin fadin albarkacin baki a Kano, inda masu sukar gwamnatin jihar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke fuskantar kame ba bisa ka’ida ba, tsarewa, barazana da cin zarafi saboda bayyana ra’ayoyinsu.

Amnesty ta ce a kusan dukkanin irin wadannan hare-haren, jami’an tsaro ne ke kame wadanda abin ya shafa ko kuma su gayyace su domin yi musu tambayoyi.

Ta ce an kuma gurfanar da wasu cikin gaggawa bisa zarge-zargen da ba su da tushe, sannan aka yanke musu hukunci cikin hanzari.

Kungiyar ta ce musamman magoya bayan jam’iyyun adawa na fuskantar irin wannan matsin lamba saboda abubuwan da suke wallafawa a kafafen sada zumunta.

Ta ce wannan yanayi na danniya da ke kara kamari a Kano na haifar da yanayin tsoro, tare da barazana ga ’yancin jama’a na fadin albarkacin baki.

Amnesty ta ce lamarin Abba Ibrahim Kofar Nasarawa, wanda aka fi sani da Aiha K Nass, na matukar tayar da hankali, saboda ya ci gaba da kasancewa a tsare tun watan Agusta.

Haka kuma, Alhaji Murtala Muhammad Dawanau na ci gaba da tsarewa ba bisa ka’ida ba saboda sharhin da ya yi a wani sakon Facebook.

Fatima Dayyabu kuwa an kama ta ba bisa ka’ida ba, aka gurfanar da ita sannan aka ci tarar ta saboda sukar gwamnati.

Sauran wadanda kungiyar ta ce sun fuskanci irin wannan cin zarafi sun hada da Maryam Usman da ake wa laƙabi da Golden Queen, Muhammad Ahmad, Hafsat Muhammad Sauwama Kauwama, Khadija Garba Kadnass, Ismail Hassan Hussain Lajin Dala da Isa Zanna Isa.

Haka kuma, Amnesty ta ce Zaidu Magaji ya fuskanci barazana da tsoratarwa mai tsanani.

Kungiyar ta ce wadannan kame-kame na nuni da yadda ake ci gaba da musgunawa ’yan siyasar adawa da magoya bayansu, tare da tsananin takura wa ’yancin fadin albarkacin baki a jihar Kano.

Amnesty ta ce ana kara amfani da jami’an tsaro wajen musgunawa da tsoratar da mutanen da ke sukar gwamna.

Ta jaddada cewa jama’a na da cikakken ’yancin sukar shugaban kasa ko gwamna, domin babu wani mutum da ya fi karfin a yi masa suka, ko da kuwa matsayinsa ya kasance mai girma.

Ta ce kama masu sukar gwamnati abu ne da ba za a amince da shi ba a cikin al’umma mai ’yanci.

Kungiyar ta kuma ce ’yancin matasan Najeriya na fadin albarkacin bakinsu na fuskantar barazana, musamman ganin yadda matasa ke fuskantar hadarin kamawa da tsarewa saboda bayyana ra’ayoyinsu masu suka a kafafen sada zumunta.

Ta bukaci gwamnatin jihar Kano da jami’an tsaro su gaggauta mutunta ’yancin jama’a na fadin albarkacin baki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata