Thursday, April 9, 2026
HomeSiyasaPDP tsagin Wike ta yi watsi da ganawar su Tanimu da jiga-jigan...

PDP tsagin Wike ta yi watsi da ganawar su Tanimu da jiga-jigan ADC

Wani ɓangare na jam’iyyar PDP da ke goyon bayan Nyesom Wike ya buƙaci mambobinsa da su yi watsi da wata ganawa da aka yi tsakanin wani ɓangare na jam’iyyar da ‘yan ADC.
Jaridar Premium Times ta ruwaito sakataren yaɗa labarai na ƙasa na ɓangaren PDP, Jungudo Mohammed, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya ce jam’iyyar ba ta amince da wannan ganawa ba kuma ba ta ba da wani izini ba.
Ya ƙara da cewa duk waɗanda suka halarci ganawar ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki sun yi hakan ne a raɗin kansu, ba a madadin jam’iyyar ba.
Sai dai a gefe guda, an rawaito cewa ganawar ta haɗa manyan ‘yan siyasa ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, inda suka tattauna kan haɗin gwiwa gabanin zaɓen 2027.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata