DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeSiyasaICPC ta kama likitan El-Rufai bisa zargin yin karya da kuma take...

ICPC ta kama likitan El-Rufai bisa zargin yin karya da kuma take umarnin kotu

Hukumar ICPC ta sanar da kama Farfesa Bello Abubakar, likitan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, bisa zargin bayar da bayanan ƙarya da kuma amfani da damar duba lafiya wajen karya umarnin kotu.

A cikin wata sanarwa da ICPC ta fitar a shafinta na Facebook, ta ce kotu ta amince a kai El-Rufai Asibitin Ƙasa da ke Abuja domin duba lafiyarsa, amma an yi amfani da wannan damar wajen gudanar da wani taron siyasa da bai cikin abin da kotu ta amince da shi ba.

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya (ICPC) ta bayyana damuwarta kan yadda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi amfani da damar zuwa duba lafiyarsa da kotu ta amince da ita yayin da yake tsare a hannun hukumar.

A cewar ICPC, Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ware ranakun 6, 7 da 8 ga Yuli, 2026 domin sauraron shari’ar cikin gaggawa. Sai dai a ranar farko El-Rufai bai gurfana a gaban kotun ba, inda ya ce yana son ganin likitansa na kashin kansa, Farfesa Bello Abubakar.

Hukumar ta ce babu wata buƙata da aka gabatar mata tun da farko game da wannan ganawa da likita, kuma likitan ICPC ya tabbatar cewa El-Rufai bai nuna yana da wata matsalar lafiya da ke bukatar kulawar gaggawa ba, sai dai ya ce, Asia El-Rufai, wadda kuma lauya ce a shari’ar, ta buƙaci ya ga likitansa.

ICPC ta ce duk da haka ta mutunta umarnin kotu tare da kare haƙƙin wanda take tsare da shi, inda ta shirya masa zuwa Asibitin National Hospital da ke Abuja cikin tsaro.

Sai dai hukumar ta ce yayin da jami’anta ke jira a waje domin ba da damar sirrin ganawar likita, wani abokin siyasar El-Rufai, Isa Ashiru Kudan, ya wallafa hotuna a shafinsa na Facebook da misalin ƙarfe 2:00 na rana, yana cewa sun kammala ganawa da El-Rufai. A cikin hotunan akwai Farfesa Bello Abubakar da wasu mutane uku tare da El-Rufai.

ICPC ta ce wannan ya nuna cewa an yi amfani da damar zuwa asibiti domin wasu ayyuka da ba su cikin abin da kotu ta amince da shi, lamarin da ta bayyana a matsayin saɓa wa umarnin kotu.

Hukumar ta ce za ta sanar da kotu wannan abin da ta kira ƙetare umarnin kotu da El-Rufai ya yi, tare da jaddada cewa ba za ta ƙara yarda a riƙa amfani da haƙurin da take yi da waɗanda ke hannunta ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata