Bankin CBN ya ƙaryata jita-jitar yin takardar Naira 5,000 mai hoton Tinubu
Babban Bankin Nijeriya CBN ya bayyana cewa hoton da ke yawo na sabuwar takardar kuɗi Naira 5,000 ba gaskiya ba ne, yana mai kira ga jama’a da su yi watsi da shi.
A cikin wani saƙo da bankin ya wallafa a shafin Facebook, ya ce “wannan labari ƙarya ne.”
