DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeSiyasaWike ya ce burinsa a sake zaben Tinubu a 2027

Wike ya ce burinsa a sake zaben Tinubu a 2027

Ministan babban birnin tarayya Abuja (FCT), Nyesom Wike, ya sake jaddada cewa babban abin da ya sa a gaba a harkokin siyasarsa a halin yanzu shi ne tabbatar da ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarar zarcewa a babban zaɓen 2027.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala duba wasu muhimman ayyukan tituna da ake gudanarwa a faɗin babban birnin tarayyar.

Ministan ya kuma yi watsi da zarge-zargen da ake yi na cewa gamayyar ƙungiyar ‘Rainbow Coalition’ da ake alaƙanta shi da ita an kafa ta ne domin daƙile ko tarwatsa jam’iyyun siyasa da ke akwai, inda ya bayyana zargin a matsayin mara tushe. Ya jaddada cewa an kafa gamayyar ne domin haɗa kan mutane daga jam’iyyun siyasa daban-daban waɗanda ke goyon bayan gwamnatin Tinubu.

“Babban abin da ya sha min kai a yanzu shi ne ganin an sake zaɓen Tinubu a karo na biyu, kuma na bayyana hakan tun daga farko cewa zan marawa shugaban ƙasa baya da dukkan ƙarfina da ikona”, in ji Wike.

Ministan ya ce bai damu da zarge-zargen da wasu ke yi ba, amma abin takaici ne yadda wasu ke iƙirarin cewa wannan gamayya za ta ɓata tsarin siyasa, yana mai nuni da cewa gamayyar ba ta hana kowa goyon bayan wani ra’ayi daban ba, sai dai kawai tana roƙon mambobinta da ‘yan Nijeriya masu ra’ayi iri ɗaya da su goyi bayan shugaban ƙasar.

Ya kafa misali da rawar da ƙungiyar gwamnonin G5 ta taka a zaɓen 2023, inda ya tambayi dalilin da ya sa ba a tayar da jijiyoyin wuya kan cewa hakan zai tarwatsa dimukradiyya ba a wancan lokacin, yana mai cewa, “Wai a 2023 lokacin da ake da G5, me ya sa babu wanda ya yi ƙorafin cewa za ta dagula siyasa? Shin Shugaban ƙasa bai ci zaɓe ba? Ko kuwa hakan ya shafi rinjayen da APC ta samu a majalisar dokoki ta ƙasa?”

Haka kuma, Wike ya karyata raɗe-raɗin da ake yi na cewa sabon salon siyasarsa na yanzu wani shiri ne na share masa fagen tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2031.

“Mutane na son ɗaukar matsayin Allah. Da farko dai, ya kamata ka yi addu’ar ganin gobe ko jibi da rai. Idan Allah ya raya ka, a lokacin ne za ka san abin da za ka yi. A shekarar 2031 Shugaba Tinubu ba zai sake takara ba kuma zai kasance yana da ra’ayi kan wanda zai gaje shi, kuma ba zan saɓa wa ra’ayinsa ba.”

Game da ayyukan da ya duba a Abuja, Wike ya nuna gamsuwarsa da yadda aikin ke tafiya cikin inganci, yana mai bayyana cewa ana sa ran kammala su kafin babban zaɓen 2027.

Ayyukan da ya duba sun haɗa da aikin babbar hanyar Inner Southern Expressway daga Ring Road I zuwa Ring Road II, hanyoyin gefe na Southern Parkway daga yankin Gaduwa zuwa Ring Road II, da kuma hanyar da ta haɗa jami’ar Nile da Ring Road III.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata