DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeSiyasa‘Wa ke mulkin Nijeriya a yanzu?’ - Atiku

‘Wa ke mulkin Nijeriya a yanzu?’ – Atiku

Atiku Abubakar, ya kalubalanci fadar shugaban Tinubu da majalisar dokokin Nijeriya su bayyana wa ’yan Nijeriya wanda ke riƙe da madafun ikon ƙasar, biyo bayan cikar kwanaki 21 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tafi hutu ba tare da miƙa mulki a hukumance ba.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce tafiyar shugaban ƙasa da mataimakinsa Kashim Shettima zuwa ƙetare a lokaci guda ya jefa ƙasar cikin rashin tabbas na shugabanci.

Dan takarar na shugaban kasa a jam’iyyar ADC ya kafa hujja da sashe na 145 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, wanda ya tanadi cewa dole ne shugaban ƙasa ya rubuta wasiƙa ga majalisar dokoki domin bai wa mataimakinsa ikon zama muƙaddashin shugaban ƙasa idan zai tafi hutu.

A cewar Atiku, tun da Shugaba Tinubu ya fice daga ƙasar a ranar 30 ga watan Agusta kuma kwanaki 21 sun cika ba tare da an ga wannan wasiƙa ba, majalisar dokoki na da alhakin amfani da sashe na 145(2) domin miƙa wa Shettima ragamar mulki.

Tsohon mataiakin shugaban kasa ya kuma nuna damuwa kan yadda Shettima kansa yake birnin New York yana wakiltar Nijeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya, yayin da ƙasar ke fama da matsalolin tsaro da suka haɗa da mutuwar mutane 37 a hannun jami’an tsaro a Minna, da kuma tsadar man fetur da ya kai N1,500 kan kowace lita.

Sai dai a wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a ranar Litinin, mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya soki kalaman na Atiku, inda ya bayyana zarge-zargensa a matsayin marasa tushe tare da jaddada cewa Shugaba Tinubu na ci gaba da tafiyar da mulkin ƙasar daga inda yake kafin ya dawo a ƙarshen mako.

Fadar Shugaban Nijeriy ta ce Tinubu zai dawo ƙasar a karshen mako, bayan tsawaita hutun aiki da ya tafi domin yi da wasu ƴan kwanaki, kamar yadda Bayo Onanuga, mai ba shugaban shawara kan harkokin yaɗa labarai ya sanar.

Fadar shugaban ƙasar ta ce duk da yana hutu, shugaban yana ci gaba da tafiyar da harkokin mulkin ƙasar, ciki har da bayar da umarnin kafa kwamiti mai zaman kansa domin binciken mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 da suka mutu a hannun jami’an tsaron NSCDC a Minna.

Sanarwar ta ce a halin yanzu, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, zai ci gaba da wakiltar shugaban ƙasa a tarurrukan cikin gida, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya tafi birnin New York domin gabatar da jawabin Nijeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata