DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeSiyasaRikicin cikin gida na barazana ga APC a jihar Kano gabanin 2027

Rikicin cikin gida na barazana ga APC a jihar Kano gabanin 2027

Wata kungiyar siyasa mai suna APC Concern for Victory Forum ta aika budaddiyar wasika ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tana mai kira gare shi da ya gaggauta magance rikicin cikin gida da ke neman kunno kai a kananan hukumomin Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa, domin kauce wa barazana ga zaben 2027.

A cikin wasikar, kungiyar ta yi zargin cewa wasu masu rike da mukaman siyasa na kokarin haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar APC, tare da zargin cewa ana hada kai da wasu domin tunzura zanga-zanga da kuma bata sunan wasu ‘yan jam’iyyar da suka bayar da gudunmawa a baya.

Kungiyar ta yi gargadin cewa idan ba a dauki mataki ba, rikicin na iya haifar da raunin jam’iyyar, rage kwarin gwiwar magoya baya da kuma bai wa ‘yan hamayya damar cin gajiyar rikicin, lamarin da zai iya shafar nasarar APC a zaben 2027.

Wasikar wadda Shugaban kungiyar Muhammad K. Muhammad da Sakataren ta BS Jameel suka sanya wa hannu, ta bukaci Gwamnan da ya binciki lamarin tare da daukar matakan tsawatarwa, ya kuma umarci shugabannin jam’iyya na jiha su warware matsalar cikin gaggawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata