Gwamnatin Nijeriya ta rage harajin shigo da motoci, shinkafa da wasu muhimman kayayyaki a cikin sabon tsarin kasafin kuɗin 2026, matakin da ya janyo muhawara daga masana tattalin arziki da masu ruwa da tsaki.
Ministan Kuɗi na Nijeriya, Wale Edun, ne ya sanar da hakan, inda ya ce an yi gyaran ne domin rage tsadar rayuwa da bunƙasa kasuwanci da kuma ƙarfafa masana’antu a faɗin kasar.
Sabon tsarin ya nuna cewa an rage harajin shinkafa daga kashi 70 zuwa 47.5, yayin da aka kuma sauƙaƙa wasu kuɗaɗen haraji kan kayayyaki da injinan masana’antu domin karfafa samar da kayayyaki a gida.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa wannan mataki na iya taimakawa wajen rage farashin kayayyaki, musamman abinci, wanda zai kawo sauki ga talakawa da ke fama da tsadar rayuwa.
Sai dai wasu sun gargaɗi cewa rage harajin na iya jawo karin shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje, lamarin da zai iya cutar da manoma da masana’antun cikin gida da ke kokarin habaka.
Haka kuma, an nuna damuwa cewa wannan tsari na iya rage kudaden shiga na gwamnati daga haraji, duk da cewa an tanadi wasu sabbin haraje-haraje domin cike gibin.
A ƙarshe, masana sun jaddada cewa nasarar wannan tsari za ta dogara ne da yadda gwamnati za ta inganta tsaro, samar da kayayyakin more rayuwa da kuma tallafawa masana’antu domin su iya gogayya da na kasashen waje.
