DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 14, 2026
HomeSiyasaTaron ADC zai gudana yau komai rintsi -Dino Melaye

Taron ADC zai gudana yau komai rintsi -Dino Melaye

Tsohon Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya tabbatar da cewa jam’iyyar ADC za ta gudanar da babban taronta na ƙasa a ranar Talata, duk da dambarwar wurin gudanar da taron a Abuja.

Melaye ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Rainbow Event Centre, inda ya ce jam’iyyar ta riga ta biya kuɗin wajen tare da ƙulla yarjejeniya, don haka babu abin da zai hana ta gudanar da taron.

Tun da farko, kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya zargi Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da Hukumar Ci-gaban Babban Birnin Tarayya FCDA da ƙoƙarin hana yin amfani da wurin taron ta hanyar matsin lamba ga mai mallakin wurin.

Sai dai Melaye ya ce jam’iyyar ba za ta ja da baya ba, yana mai jaddada cewa suna da yarjejeniya sahihiya da masu wurin, kuma za su gudanar da taron kamar yadda aka tsara.

A ɗayan ɓangaren kuma, Wike ya musanta zargin, yana cewa bai san da wata buƙata da aka gabatar ba, tare da jaddada cewa wurare kamar su Eagle Square kowa zai iya amfana dashi matuƙar an bi ƙa’idar da aka shimfiɗa.

Lamarin na zuwa ne a dai-dai lokacin da rikicin cikin jam’iyyar ADC kan shugabanci ke ci gaba da ƙamari, yayin da ɓangarorin daban-daban ke ƙoƙarin tabbatar da tasirinsu gabanin babban taron.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata