An yanke wa ɗan siyasar Afirka ta Kudu Julius Malema hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari bayan samunsa da laifin harba bindiga a wani taron siyasa da aka gudanar tun shekarar 2018.
Wannan hukunci ya fito ne daga wata kotu a ƙasar, inda alkali ya bayyana cewa aikinsa ya saba doka kuma ya jefa jama’a cikin haɗari.
Malema, wanda shi ne jagoran jam’iyyar Economic Freedom Fighters, ya harba bindiga ne a sama yayin wani gangami a filin wasa a yankin Eastern Cape. Bidiyon wannan lamari ya bazu sosai a lokacin, lamarin da ya jawo cece-kuce da kuma bincike daga hukumomi.
Kotun ta same shi da laifuffuka da dama da suka haɗa da mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba, harba bindiga a bainar jama’a, da kuma jefa rayuwar mutane cikin haɗari.
Alkalin da ya yanke hukuncin ya jaddada cewa matsalar tashin hankali da bindiga a Afirka ta Kudu babbar matsala ce, don haka dole ne a ɗauki mataki mai tsauri kan irin wannan hali.
A lokacin shari’ar, Malema ya musanta zargin, yana mai cewa bindigar da aka gani kamar wasa ce, kuma harbin da ya yi wani bangare ne na murnar taron.
Sai dai kotu ta yi watsi da wannan hujja, tana mai cewa abin da ya aikata ba wasa ba ne, illa karya doka.
Rahotanni sun nuna cewa lauyoyinsa sun garzaya da shigar da ƙorafi domin ɗaukaka ƙara nan take bayan yanke hukuncin, suna fatan kotu mafi girma za ta sake duba shari’ar.
Idan har hukuncin ya tabbata bayan dukkan matakan ɗaukaka ƙara, zai iya rasa kujerarsa ta majalisa, wanda hakan zai zama babban koma baya ga jam’iyyarsa.
