DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, April 15, 2026
HomeSiyasaAn fara kiraye-kiraye ga Goodluck Jonathan ya sake fitowa takara a 2027

An fara kiraye-kiraye ga Goodluck Jonathan ya sake fitowa takara a 2027

Ana ci gaba da samun kiraye-kiraye ga tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, da ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, yayin da ake fuskantar sauye-sauye dalilin zuwan haɗakar siyasa a cikin jam’iyyun adawar ƙasar.

Jonathan ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙasa ga marigayi Umaru Musa Yar’Adua daga shekarar 2007, har zuwa rasuwarsa a watan Mayun 2010, inda daga nan aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.

Daga bisani, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2011, amma ya sha kaye a yunƙurinsa na zarcewa a 2015 bayan ya fuskanci tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata