DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, April 16, 2026
HomeLabaraiKotu ta ba da umurnin kama tsohuwar ministar jin kai ta Nijeriya...

Kotu ta ba da umurnin kama tsohuwar ministar jin kai ta Nijeriya Sadiya Umar Farouq

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarƙashin mai shari’a Jude Onwuegbuzie, ta bayar da umarnin kama tsohuwar Ministar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci ta Nijeriya, Sadiya Umar Farouq, tare da tsohon Babban Sakatare a ma’aikatar, Bashir Nura Alkali, bayan sun gaza halartar zaman kotu da aka shirya domin gurfanar da su a ranar Alhamis.

Rahotanni sun nuna cewa an shirya gurfanar da su ne a gaban kotu a wani zaman shari’a da Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin Nijeriya tu’annati ke tuhumarsu da laifuka 21 da suka shafi cin amanar ofis, amfani da mukami ba bisa ƙa’ida ba, da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati, a zargin badakalar kudade da ta kai dala miliyan 1.3 da kuma Naira miliyan 746.6.

A lokacin zaman kotu, lauya mai gabatar da ƙara, Rotimi Jacobs, SAN, ya bayyana cewa an shigar da ƙarar tun a watan Disamba 2025, amma ba a samu damar gurfanar da waɗanda ake tuhuma ba saboda rashin halartar su.

Ya ce duk da cewa an bai wa lauyoyinsu dama su tabbatar da zuwansu, hakan bata samu ba har zuwa lokacin da aka sa hannu kan umarnin kotu na tilasta gabatar da su, kamar yadda hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook.

Sai dai lauyan Sadiya Umar Farouq, Abdul Ibrahim, SAN, ya shaida wa kotu cewa rashin halartar ta ya samo asali ne daga rashin lafiya, yana roƙon kotu ta karɓi takardun da suka gabatar a matsayin hujja. Amma kotun ta ƙi amincewa da wannan buƙata.

Haka kuma, EFCC ta nemi kotu ta sauya wani buƙatar da ta gabatar a baya domin ƙara matakan kama waɗanda ake tuhuma, tana mai cewa akwai hujjoji da ke nuna cewa sun ki bayyana a kotu duk da an yi musu sammaci.

Bayan sauraron hujjojin bangarorin biyu, mai shari’a Onwuegbuzie ya amince da bukatar EFCC, inda ya bayar da sammacin kama Sadiya Umar Farouq da Bashir Nura Alkali.

Ya kuma daga shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Mayu, 2026 domin ci gaba da zaman shari’ar bayan gurfanar da su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata