Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya dakatar da tallafin kuɗi na Naira miliyan 150 da gwamnatin jihar ke bai wa kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric a kowanne wata.
An bayyana wannan mataki ne a wani taro da aka gudanar tsakanin gwamnatin jihar, shugabannin kamfanin da kuma sauran masu ruwa da tsaki a Birnin Kebbi, inda gwamnan ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ake samar da wutar lantarki a jihar.
Gwamna Idris ya ce wannan shawara ta biyo bayan koke-koken da ‘yan kasuwa da mazauna jihar suka dade suna yi kan rashin isasshiyar wutar lantarki, duk da irin tallafin da gwamnati ke bayarwa ga kamfanin.
Ya bayyana cewa duk da wannan kuɗi da ake kashewa kowane wata, babu wani gagarumin sauyi da aka gani a bangaren samar da wuta.
A cewarsa, gwamnatin jihar ba za ta ci gaba da kashe irin wannan makudan kuɗaɗe ba tare da ganin ingantaccen sakamako ba.
Don haka ne ya yanke shawarar dakatar da tallafin tare da neman wasu hanyoyin samar da wutar lantarki mafi inganci ga al’ummar jihar.
