Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya kare shugaban hukumar zaɓen Nijeriya INEC, Joash Amupitan, kan zargin nuna goyon baya a wani shafi na sada zumunta.
Takaddamar ta samo asali ne daga wani sako da aka ce an wallafa a shafin X wadda ake zargin Amupitan da nuna goyon baya ga wata jam’iyya, lamarin da ya janyo zarge-zarge kan rashin tabbacin sahihancin zabukan 2027.
Sai dai Akpabio ya ce an dauki sakon ba daidai ba, yana mai jaddada cewa bai ambaci wata jam’iyya ba, kuma an wallafa shi ne kafin Amupitan ya zama shugaban INEC, lokacin da yake malamin jami’a.
Ya kara da cewa duk da haka, duk wanda ke rike da mukamin gwamnati dole ne ya kasance mai nuna adalci da rashin bangaranci, domin kare amincewar jama’a ga tsarin zabe.
