DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 21, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya ta gurfanar da mutane shida da ake zargi da kitsa...

Gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da mutane shida da ake zargi da kitsa juyin mulki

Gwamnatin Nijeriya ta shigar da ƙara mai ƙunshe da tuhume-tuhume guda 13 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan wasu da ake zargi da kitsa juyin mulki domin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

Daga cikin waɗanda ake tuhuma akwai tsohon Manjo Janar Mohammed Gana, tsohon Kyaftin na ruwa Erasmus Victor, jami’in ‘yan sanda sufeto Ahmed Ibrahim, da wasu uku, Zekeri Umoru, Bukar Goni da Abdulkadir Sani.

Haka kuma, an ambaci tsohon ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo a cikin shari’ar.

Takardar tuhumar da ofishin Babban Lauyan Tarayya ya shigar, ta zargi waɗanda ake tuhuma da laifukan da suka haɗa da cin amanar ƙasa, ta’addanci, ɓoye bayanan tsaro, da kuma safarar kuɗaɗen da ke da alaƙa da tallafa wa ta’addanci.

Ana zargin cewa a shekarar 2025 sun haɗa baki domin tayar da tarzoma da nufin kifar da gwamnati, lamarin da doka ta tanadi hukunci mai tsauri a kansa.

Har ila yau, ana zargin wasu daga cikinsu da sanin shirye-shiryen aikata wannan laifi amma suka kasa sanar da hukumomi ko ɗaukar matakan hana aukuwar sa.

Bugu da ƙari, ana tuhumar wasu da karɓa da adana kuɗaɗen da ake zargin na tallafa wa ta’addanci, ciki har da miliyoyin naira da aka ce sun samu ba bisa ƙa’ida ba kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata