DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 20, 2026
HomeLabaraiKotu ta karɓi hujjojin EFCC kan wasu zarge-zarge da take yi wa...

Kotu ta karɓi hujjojin EFCC kan wasu zarge-zarge da take yi wa Malami

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta karɓi hujjoji guda tara a shari’ar zargin badakalar kuɗaɗe da ake yi wa tsohon Ministan Shari’a na Nijeriya Abubakar Malami tare da matarsa da ɗansa.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik, ta amince da karɓar takardun ne bayan da hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa ta gabatar da su, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ana tuhumar Malami da iyalansa da laifuka guda 16 da suka haɗar da haɗin baki, ɓoye kuɗaɗe, da halasta kudaden haram da suka kai kusan Naira biliyan 8.7.

Takardun da kotun ta karɓa sun haɗa da bayanan banki da suka shafi asusun da ake dangantawa da waɗanda ake tuhuma da kuma wasu kamfanoni.

An gabatar da su ne ta hannun wani jami’in banki wanda ya bayyana cewa ya karɓi buƙata daga EFCC domin samar da bayanan da suka shafi binciken.

Shaidar ya kuma bayyana cewa takardun sun ƙunshi bayanai kan mu’amaloli da suka gudana tsawon shekaru da dama, ciki har da manyan kuɗaɗe da aka tura zuwa asusun da ake bincike.

Lauyan waɗanda ake tuhuma ya yi ƙoƙarin ƙalubalantar karɓar wasu daga cikin takardun, musamman saboda kwanakin da aka rubuta su, amma kotun ta yi watsi da ƙorafin tare da amincewa da su a matsayin hujja.

Bayan kammala sauraron shaidar, lauyan ɓangaren kariya ya nemi a ba shi lokaci domin nazarin hujjojin da aka gabatar kafin fara tambayar shaida, kuma kotun ta amince da hakan.

Daga ƙarshe, kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Mayu, 2026, domin ci gaba da shari’ar da kuma gabatar da ƙarin hujjoji da tambayoyi daga ɓangarorin biyu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata