DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 21, 2026
HomeKasuwanciNijeriya ta fara fitar da fetur zuwa waje karo na farko bayan...

Nijeriya ta fara fitar da fetur zuwa waje karo na farko bayan aikin matatar Dangote

Nijeriya ta kafa tarihi bayan ta koma mai fitar da man fetur da aka tace zuwa ƙasashen waje, maimakon yadda aka saba na fitar da ɗanyen mai da shigo da fetur.

Wannan sauyi ya biyo bayan ƙaruwar samar d man daga matatar Dangote da ke Lekki a jihar Legas, wadda ke fitar da kusan ganga 44,000 na fetur a kullum a watan Maris.

Rahoton TRT Afrika ya nuna cewa shigo da fetur ya ragu zuwa kusan ganga 41,000 a rana a wannan lokaci, wanda shi ne mafi ƙanƙanta da aka taba samu.

Ana danganta wannan sauyi da karuwar samarwa daga matatar, inda duk wani ƙarin mai da aka tace ake fitar da shi zuwa ƙasashen waje.

Matatar Dangote tana da ƙarfin tace ganga 650,000 na ɗanyen mai a rana, kuma a watan Maris ta sarrafa kusan ganga 565,000, ɗaya daga cikin mafi girman adadin da ta taba kaiwa tun bayan fara aiki.

Nijeriya dai ta dade tana dogaro da shigo da fetur saboda rashin isassun matatun mai, duk da kasancewarta babbar mai fitar da ɗanyen mai a Afirka.

Ana sa ran wannan sabon ci gaba zai taimaka wajen biyan buƙatun cikin gida gaba ɗaya, tare da ƙara kuɗaɗen shiga ta hanyar fitar da fetur zuwa ƙasashen waje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata