A sake gano wata sabuwar cutar COVID-19 a Nijeriya, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito.
Rahoton ya ce an samu cutar ne a Jihar Cross River, inda wani ɗan ƙasar China mai shekaru 53, da ke aiki da kamfanin Lafarge, ya kamu da cutar.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Henry Ayuk, ya bayyana cewa mutumin ya shigo Nijeriya a ranar 17 ga Maris, kafin daga bisani ya fara nuna alamun rashin lafiya.
Ya ce an fara kula da shi a wani asibiti kafin daga baya aka mayar da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Calabar (UCTH) domin ƙarin kulawa.
A cewarsa, an ɗauki samfurinsa tare da bin duk ƙa’idojin gwaji, sannan aka tabbatar da cewa yana ɗauke da cutar COVID-19.
Sai dai ya tabbatar da cewa halin lafiyar marar lafiyan na inganta, yana mai cewa babu dalilin daga hankali.
Ayuk ya ƙara da cewa ma’aikatar lafiya ta jihar ta shirya tsaf domin dakile kowanne irin ɓarkewar cutar, tare da inganta tsarin sa ido da kariya.
A nata ɓangaren, jami’ar kula da cututtuka ta jihar, Dakta Inyang Ekpenyong, ta ce a riga an fara bin diddigin mutanen da suka yi mu’amala da wanda ya kamun.
Ta bayyana cewa an farfado da cibiyar gaggawa tare da tura tawagar kula da annoba zuwa yankin Akamkpa domin shawo kan lamarin.
Ita ma wakiliyar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a jihar, Dakta Yewande Olatunde, ta jaddada cewa cutar na nan, tare da kira ga jama’a da su cigaba da bin matakan kariya.
