DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 21, 2026
HomeLabaraiRadda ya ɗaga matsayin albashin Hakimai da Dagattai a Katsina

Radda ya ɗaga matsayin albashin Hakimai da Dagattai a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da ɗaga Albashin hakimai zuwa mataki na 16 (GL 16) da Dagattai zuwa mataki na 10 (GL 10) a faɗin jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Ibrahim Kaula ya fitar, inda yace wannan shine ya zama farkon aiwatar da sabon tsarin ƙarƙashin dokar masarautu da majalisar dokokin jihar ta amince da ita a watan Agustan 2025.

Gwamnan ya bayyana matakin a matsayin babban ci gaba wajen ƙarfafa tsarin sarakunan gargajiya da inganta jin daɗinsu.

Ya kuma yabawa Hukumar Kula da Kananan Hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da aiwatar da shirin.

Radda ya gode wa sarakunan gargajiya bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bai wa gwamnati, yana mai cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Ya kuma buƙaci a ci gaba da haɗin kai da addu’a domin magance matsalolin da ke fuskantar al’umma.

Gwamnan ya nuna gamsuwa da yadda tsaro ya inganta a jihar, inda ya danganta hakan da haɗin gwiwar gwamnati, jami’an tsaro da shugabannin al’umma.

Tun da farko, mai ba gwamna shawara kan harkokin masarautu, Usman Abba Jaye, ya ce shirin wani muhimmin mataki ne na sake farfaɗo da martabar sarakunan gargajiya.

Shi ma shugaban Hukumar kula da Kananan Hukumomi, Usman Mamman Maska, ya ce an bi dukkan matakan doka wajen aiwatar da shirin, yana mai cewa zai taimaka wajen ƙarfafa shugabanci a matakin ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata